Kotu ta bada belin mahaifiyar Maryam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijin ta

Kotu ta bada belin mahaifiyar Maryam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijin ta

- Kotu ta ba da belin Mahaifiyar Maryam Sanda

- An bayar da belin nata ne kan kudi naira miliyan 10

- Har ila yau kotu ta bukaci mutane biyu su tsaya mata

Wata babban kotu dake Abuja karkashin jagoranci mai shari’a Mairo Nasir, ta ba da belin Maimuna Aliyu a kan kudi naira miliyan 10.

Ana zargin Maimuna, wacce ta kasance ce tsohuwar Shugabar Aso Savings and Loan, plc da zambar kudi naira miliyan 57 a lokacin da ta ke aiki tare da hukumar Aso Savings.

Idan za ku tuna, ita dai ce a wata kotun kuma ta ke fuskantar tuhuma dangane da zargin da ake yi wa ‘yar ta Maryam Sanda da kashe mijin ta, Bilyaminu Halliru.

Kotu ta bada belin mahaifiyar Mayam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijin ta
Kotu ta bada belin mahaifiyar Mayam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijin ta

Kuliyar kotun Mairo ta ba da belin ta bayan da lauyan ta, Joe-Kyari Gadzama ya bukaci a ba da belin na ta.

KU KARANTA KUMA: Jami'an ICPC sun yi ram da Mahaifiyar Maryam Sanda bisa zargin satar kudi

Ta kuma bukaci mutane biyu da su tsaya mata, wadanda dole su kasance mazauna babban birnin tarayya Abuja ne, sannan lallai sai sun je kotun sun yi rantsuwar iyar gaskiyar aiki ko sana’ar da su ke yi su na samun kudi.

An dage shari’ar sai ranar 12 Ga Maris, 2019 domin a fara sauraren ba’asin karar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng