Rikicin Benuwe: Idan gwamnati ba za ta iya kare mu, za mu kafa namu sojojin - Unongo
- Shugaban Kabilan Tibi, Wantaregh Unongo ya ce al'ummar jihar za su kafa rundunar sojojin da za su kare kansu idan gwamnatin tarayya ta gaza
- Shugaban ya ce al'ummar Tibi na cikin wadanda suka sadaukar da rayuwar su lokacin yakin basasar Najeriya domin ganin kasar nan ta zauna lafiya
- Tsohon gwamna a zamanin mulkin soja, Manjo Janar Lawrence Onoja ya yi kira da gwamnati ta maimaita irin aikin da tayi na 'Operation Python Dance' na kwantar da tarzoma a sashin kudu maso gabas
Wani shugaban kabilan Tibi kuma Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa, Wantaregh Unongo ya ce idan Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa sauke nauyin da ya rataya a kan sa na kare lafiya da dukiyoyin al'ummar Benuwe, toh mutanen za su horas da na su sojojin domin su kare kansu.

Unongo ya tunatar da al'umma cewa dimbin al'ummar kabilat Tibi suna daga cikin wadanda suka bada rayyukan su a yakin basasar Najeriya domin ganin an samu tabbaticiyar zaman lafiya da hadin kai. Saboda haka ba daidai bane a sa ido ana ganin ana yi musu kisan kiyashi.
DUBA WANNAN: Bamu da lokaci, ku gaggauta sakin kasafin kudin bana - Fadar shugaban kasa ta fadawa 'yan majalisa
"Idan Gwamnatin Tarayya ta gaza tsayar da hare-haren ko kuma kamo wandanda ke kai harin cikin makonni biyu, toh mu zamu kafa rundunar sojin namu domin mu kare kan mu. Ba za mu yarda wasu suyi mana mulkin malaka ba, zamu iya mulkar kan mu." inji Unongo.
A yayin da yake tofa albarkacin bakin sa kan lamarin, Tsohon gwamnan mulkin soja na jihohin Filato da Katsina, Manjo Janar Lawrence Onoja (murabus) ya bayyana hare-haren a matsayin kisan kare dangi, ya kuma ce dole ne a kawo karshen kashe-kashen.
Onoja ya yi kira da Gwamnatin Tarayyah ta maimaita irin abin da tayi a yankin kudu maso gabashin Najeriya inda ta aike sojojin Najeriya suka kwantar da tarzoman karkashin shirin 'Operation Python Dance'. Ya kuma yi kira da al'ummar jihar su cigaba da bawa Gwamna Orthom goyon baya domin tabbatar dokar hana kiwo a fili a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng