Jami'an ICPC sun yi ram da Mahaifiyar Maryam Sanda bisa zargin satar kudi
- Ana zargin Mahaifiyar Maryam Sanda da satar wasu Miliyoyi
- Akwai kudin fili har na Miliyan 57 da su ka bace a hannun ta
- Babban Lauya Gadzama ya nemi a bada belin Maimuna Aliyu
Mahaifiyar wata Mata da aka yi ta ce-ce-ku-ce a kan ta kwanaki bayan da aka zarge ta da kashe Mijin ta watau Maryam Sanda ta shiga hannun Hukumar ICPC bisa zargin cin wasu kudi. Lauyan ta Joe Kyari Gadzama ya nemi beli.
Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta damke Maimuna Aliyu bisa zargin yin gaba da wasu kudin fili da ta saida na Kamfanin Aso Savings a Yankin Jabi da ke Birnin Abuja amma ta yi gaba da kudin har Naira Miliyan 57.
KU KARANTA: Wasu Samari sun lakadawa wani Soja dan-banzan duka
Ana kuma zargin Maimuna Aliyu da shaidar zur a wajen binciken wannan kudi da ake zargi ta sace amma ta tubure cewa ta maidawa Kamfanin kudin filayen. Hajiya Maimuna ta musanya zargin da ke kan ta inda ta nemi a bada belin ta.
Maimuna Aliyu ta bakin Lauyan ta tayi kukan cewa yanzu haka tana da 'Diya da jikar da ta ke kula da su wanda ke garkame a gidan yari don haka za ta nemi a sake ta. Maimuna ta rike Darekta a Kamfanin nan na Aso Savings kwanakin baya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng