Yanzu-yanzu: 'Yar jarida ta raunata wani dan sanda yayin zanga-zangan ma'aikata a Kaduna
- Motar wata 'yar jarida ta kwace, ta kutsa cikin dandazon 'yan sanda a wurin zanga-zangan ma'aikata a Kaduna
- 'Yar jaridar ta ce ta rikice ne
- Ma'aikata a Kaduna na gudanar da zanga-zangar korar malaman makarantar firamare 22,000
Motar wata 'yar jarida, Hajiya Ummulkhairi, ta kutsa cikin ayarin 'yan sanda bayan da ta kwace daga hannun ta.
An samu yawaitar jami'an tsaro yau a kan titunan garin Kaduna domin su hana zanga-zangar nuna adawa da korar malaman makarantar firamare da ma'aikatan jihar da kungiyar kwadago ke gudanarwa.
Motar 'yar jaridar, kirar Peugeot 307, ta kwace daga hannun 'yar jaridar yayin da take dosar ofishin gidan talabijin na kasa (NTA) wanda kuma yake makwabtaka da ofishin kungiyar kwadago na jihar Kaduna. 'Yar jaridar ta ce ta rude ne a lokacin da ta ci karo da dandazon masu zanga-zangar kuma motar ta kwace mata ne a daidai lokacin da take kokarin shan wata kwana domin gujewa dubban mahalarta zanga-zangar da suka rufe hanyar da take kai.
DUBA WANNAN: Hatsari ba sai a mota ba: Jirgi ya kife da 'yan ci-rani 200 daga Najeriya da wasu kasashen Afrika
Bayan ta kasa sarrafa motar ne sai ta kutsa kai cikin ayarin jami'an tsaro da suka hada da jami'an soji da na 'yan sanda, kuma nan take ta raunata wani dan sanda tare da dukan wasu motoci biyu; motar 'yan sanda da wata motar kirar Peugeot 406 mallakar wani dan jarida dake aiki da Leadership Hausa.
An dauke motocin da hatsarin ya shafa daga wurin da abin ya faru.
Rahotanni basu bayyana yanayin raunin da dan sandan ya samu ba.
Ma'aikatan da 'yan kungiyar kwadago na cigaba da gudanar da zanga-zangar duk da kasancewar jami'an tsaro da gwamnatin jihar ta jibge domin dakatar da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng