Gani ya kori ji: Dubi yadda kungiyar kwadago da ma'aikata ke gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna

Gani ya kori ji: Dubi yadda kungiyar kwadago da ma'aikata ke gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna

- Malaman makaranta sun shiga yajin aiki a jihar Kaduna

- Sun fara gudanar da zanga-zangar adawa da korar ma'aikata a jihar

- Gwamnatin jihar ya ce babu gudu, babu ja da baya a kokarinta na tsaftace harkar ilimi

Dangantaka tsakanin malaman makarantun firamare da gwamnatin jihar Kaduna ta fara tsami ne tun bayan da gwamnatin jihar ta bayyana cewar za ta kori malamai 22,000 saboda sun gaza cin jarrabawar gwaji da gwamnatin ya yi masu.

Gani ya kori ji: Dubi yadda kungiyar kwadago da ma'aikata ke gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna
kungiyar kwadago da ma'aikata na gudanar da zanga-zanga a Kaduna

Gani ya kori ji: Dubi yadda kungiyar kwadago da ma'aikata ke gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna
kungiyar kwadago ta ce babu gudu, babu ja da baya a kan zanga-zanga a jihar Kaduna

Ana cikin wannan dambaruwa ne sai kungiyar kwadago ta zargi gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i da korar ma'aikata kimanin 36,000 cikinsu harda malaman makarantun firamare 22,000.

DUBA WANNAN: Zargin makiyaya da kisan mutum 33 ya jawo barkewar zanga-zanga a Benuwe

Tun farkon satinnan ne malaman makarantun suka shiga yajin aiki kafin daga bisani su fara zanga-zanga da hadin gwuiwar kungiyar kwadago.

Gani ya kori ji: Dubi yadda kungiyar kwadago da ma'aikata ke gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna
kungiyar kwadago da ma'aikata na gudanar da zanga-zanga a Kaduna

Saidai gwamnatin jihar Kaduna ta ce ba zata janye yunkurin da take yi na kawo gyara a makarantun gwamnati da 'ya'yan talakawa ke halarta ba.

Gani ya kori ji: Dubi yadda kungiyar kwadago da ma'aikata ke gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna
kungiyar kwadago da ma'aikata na gudanar da zanga-zanga a Kaduna

NLC ta ce jibge jami'an tsaro a titunan garin da gwamnatin jihar ta yi na zai ba ta tsoro ba, ko ya saka ta fasa gudanar da zanga-zanga ba.

Gani ya kori ji: Dubi yadda kungiyar kwadago da ma'aikata ke gudanar da zanga-zanga a jihar Kaduna
Jami'an tsaro a kan titi a Kaduna

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng