Bugun Zuciya: Rashin lafiyar El-Zakzaky ta cigaba da tsananta

Bugun Zuciya: Rashin lafiyar El-Zakzaky ta cigaba da tsananta

Rahotanni da sanadin jaridar The Guardian sun bayyana cewa, rashin lafiyar daurarren shugaban kungiyar shi'a ta Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tana ci gaba da tsananta inda yake fama da ciwon bugun zuciya da mutuwar ɓarin jiki.

Legit.ng ta fahimci cewa, El-Zakzaky dan shekaru 68 a duniya yana garkame tun a watan Dasumbar shekarar 2015, a sakamakon artabun mambobin kungiyarsa da dakarun sojin kasan Najeriya a garin Zaria dake jihar Kaduna.

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

Sai dai har yanzu kungiyar ta shi'a tana fusace da gwamnatin shugaba Buhari inda take cewa, daurin da ake yiwa shugabanta ya sabawa ka'ida tare da hana shugabanta samun ingantacciyar kulawar likitoci wajen duban lafiyarsa.

KARANTA KUMA: Wani mummunan hatsari ya salwantar da rayuka goma a jihar Ogun

A wata ganawa da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata, kungiyar ta bayyana cewa a halin yanzu shugabanta yana fama da matsanancin ciwon bugun zuciya da har ba ya iya motsa wasu sassan jikin sa.

Kungiyar da sanadin kakakin ta, Farfesa Abdullahi Danladi, ya bayyana cewa shugaba El-Zakzaky yana fama da ciwo da ko sallah ba ya iya tsayuwa wajen yin ta, tare da rauni na karfin muryarsa da take kyarma a halin yanzu.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng