likitocin Najeriya 38,000 suna aiki kasashen waje
- Ferfesa Muheez Durosinmi ya korafi akan yadda Najeriya ke fama da karancin likitoci asibitocin kasar
- Durosinmi ya ce likita daya yana duba mara sa lafiya 6,000 a kowani rana a Najeriya
- Rabin likitocin Najeriya suna kasahen wajen Ferfesa Muheez Durosinmi
Mataimakin shugaban jami’an Eko University of Medicine and Health Sciences, Ferfesa Muheez Durosinmi, yayi korafi akan yadda aka fama da katancin likitoci a kasar.
Durosinmi, ya ce al’amarin Najeriya yanzu ya koma likita daya yana duba mara sa lafiya 6,000 a kowani rana.
Rabim likitotcin Najeriya suna aiki a kasashen waje.
Ferfesa Muheez Durosinmi,ya bayyan haka ne lokacin da yake kaddamar da kwamitin kula da harkokin jami’an.
KU KARANTA : Yansada sun gano sabuwar sansanin fataucin dan Adam a jihar Legas da ceto yara shida
Ya ce likitoci 35,000 kadai daga cikin likitoci 75,000 da aka musu rajista a Najeriya ke aiki a cikin kasar.
Likitocin Najeriya suna samun kyakywan horo, duk kasar da likitocin Najeriya suka je suna samu kyakywan tarba.
Ferfesa Akanni Hussein, ya ce rashin kayan aiki ke sa likitocin Najeriya ke guduwa kasashen waje.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng