Matuka jirgin sama sun kaure da fada a yayin da jirgi ke tsaka da keta hazo da fasinjoji 324
- Matuka jirgin sama sun kaure da fada a cikin jirgi yayin da yake tsaka da keta hazo da fasinjoji 324
- Kamfanin jirgin ya sallami direbobin daga aiki
- Jirgin ya sauka lafiya duk da haka
Wani kamfanin jirgin sama a Indiya ya sallami wasu direbobi biyu daga aiki saboda sun kaure da fada a yayin da jirgin dake dauke da fasinjoji 324 ke tsaka da keta hazo.
Wannan lamari ya afku ne a ranar farko ta shekarar nan yayin jigilar wasu fasinjoji daga birnin Landon na kasar Ingila zuwa birnin Mumbai dake kasar Indiya.
Kamfanin jirgin (Jet Airways), a sanarwar da ya fitar ya ce har yanzu basu san mene ne ya haddasa fada tsakanin direbobin ba, illa iyaka dai sun san cewar direban jirgin namiji ne ya fara sheke direba mace da mari.
DUBA WANNAN: Isra'ila ta bawa 'yan Afrika wa'adin barin kasar ko ta garkame su a gidajen yari
"Mun sallami direbobin gaba dayansu daga aiki," a cewar kamfanin. Bayan sallamar direbobin, kamfanin bai yi wani karin bayani ba.
Kafafen watsa labarai a kasar Indiya sun ce an ga direbar jirgin mace ta fito daga dakin tukin jirgin tana kuka bayan direban jirgin namiji ya mare ta, sannan taki yarda ta koma cikin dakin tukin jirgin.
Daga bisani jirgin da yake dauke da fasinjoji 324 ya sauka lafiya kamar yadda jaridar Fox ta rawaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng