Boko Haram: Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ziyarci garin Bama (hotuna)

Boko Haram: Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ziyarci garin Bama (hotuna)

- Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta ziyarci garin Bama

- Amina Mohammed ta samu rakiyan gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima

- Ta sha alwashin mika rahoto domin tallafawa gwamnatin jihar

Rahotanni sun kawo cewa, mataimakiyar sakataren Mjalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina J Mohammed ta ziyarci garin Bama.

Tsohuwar ministar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu rakiyar Gwamna Shettima, Komishinan sake gina garuruwa da Boko Haram ta lalata da sauran jami'an gwmnatin jihar Borno.

Boko Haram: Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ziyarci garin Bama (hotuna)
Boko Haram: Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ziyarci garin Bama

Tawagar da farko ta ziyarci hedikwatar Sojoji ta 21 dake garin Bama, inda daga bisani ta gana da wasu 'yan gudun hijira dake Science Bama. wanda ke dauke da 'yan gudun hijira sama da dubu goma sha biyar (15,000).

Boko Haram: Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ziyarci garin Bama (hotuna)
Tsohuwar ministar ta samu rakiya gwamnan jihar Borno

Daga karshe Amina ta yi alkawarin nika rahoto da zummar magance matsaloli da taimakawa gwmnatin Jihar don kawo karshe mawuyacin halin da al'ummar wannan yanki ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hawaye na kwaranya yayinda dubban mutane sun halarci taron karrama wadanda harin makiyaya ya cika da su a Benue (hotuna)

Boko Haram: Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ziyarci garin Bama (hotuna)
Boko Haram: Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ziyarci garin Bama

Idan ba'a manta ba Gwamnatin Borno tace ta gina gidaje dubu goma sha daya da azuwan karatu 170 duk da zumar mayar da barna da Boko Haram tayi a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng