Hatsari ba sai a mota ba: Jirgi ya kife da 'yan ci-rani 200 daga Najeriya da wasu kasashen Afrika

Hatsari ba sai a mota ba: Jirgi ya kife da 'yan ci-rani 200 daga Najeriya da wasu kasashen Afrika

- Jirgi ya kife da 'yan ci-rani 200 daga Najeriya da wasu kasashen Afrika

- Wasu sun tsira da ransu

- Har yanzu ba'a ga wasu kimanin mutane 100 ba

Shekarar 2018 ba ta farawa masu dabi'ar nan ta tafiya yawon ci-ranizuwa kasashen ketare, musamman Turai, a sa'a ba, domin wani jirgin ruwa dauke da 'yan ci-ranin ya kife da su a tsakiyar teku yayin da suke kokarin tsallakawa ya zuwa kasashen Italiya Sifen.

Jami'in kungiyar kare 'yan ci-rani ta duniya (IOM) a kasar Libiya, Christine Petre, ya tabbatar da afkuwar hatsarin tare da bayyana cewar 'yan ci-ranin sun tashi ne daga tashoshin jiragen ruwa dake garuruwan Azzawiyah da Al Khums a kasar Libiya.

Hatsari ba sai a mota ba: Jirgi ya kife da 'yan ci-rani 200 daga Najeriya da wasu kasashen Afrika
Hatsari ba sai a mota ba: Jirgi ya kife da 'yan ci-rani 200 daga Najeriya da wasu kasashen Afrika

"Yawancin wadanda suka tsira da ransu 'yan kasashen Afrika ne da suka hada da Senegal, Mali, da Najeriya. Akwai mutane takwas daga kasar Bangladesh da kuma mutane biyu daga Pakistan," a cewar Petre.

DUBA WANNAN: Jiragen ruwa 34 makare da man fetur da kayan abinci sun fara isowa Legas

Petre ya kara da cewar har yanzu akwai wasu mutane 100 da suka bace, ba'a gansu ba.

A jiya, Laraba, shugaban kungiyar​ IOM a kasar Libiya, Othman Belbesi, ya bayyana cewar a kalla 'yan ci-rani 200 sun mutu ko kuma sun bace bayan da jirginsu ya kife a teku ranar Asabar.

Kazalika ya ce a kalla mutane 800 aka tserar daga mutuwa bayan kifewar jirginsu a kwanaki goman farkon sabuwar shekarar nan.

Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai kula da masu yawon ci-rani ya yi alkawarin tallafawa wadanda suka tsira da ransu a wannan sabon hatsari da ya faru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng