Sojojin sun kama wani sojan gona yayin da yake cin zalin jama’a a Legas (Hotuna)
Jami’an Bataliyar rundunar Sojin Najeriya na 174 sun yi nasarar cafke wani bata gari dake yin Sojan gona a yayin dayake cin zarafin jama’a a unguwar Isawo na jihar Legas.
Kaakakin rundunar na kasa, Birgediya Sani Usman Kukasheka ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar a ranar Laraba 10 ga watan Janairu, inda yace jami’an Soji sun kama mutumin ne, Pascal Philip sanye da kayan Sojoji.
KU KARANTA: Yadda wasu mutane suka halaka wani jami’in leƙen asiri na hukumar EFCC
Kaakaki SK yace dubun Sojan gonan ya cika ne a ranar Talata 8 ga watan Janairu a lokacin dayake tsaka da cin zarafin jama’an unguwar Isawo dake unguwar Ikorodu na jihar.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya da cin zarafin jama’a, har kudi Pascal yake kwace musu. Sai dai a yanzu Kaakakin rundunar yace suna gudanar da binciken a kan Sojan gonan, kuma da zarar sun kammala, zasu mika shi ga Yansanda.
Daga karshe Birgediya Kukasheka ya bukacin jama’a da su dinga taimaka ma hukumomin tsaro da bayanai sahihai game da duk wani sojan gona da suka gani, musamman masu bata ma hukumomin tsaro suna.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng