Mummunar hatsarin mota a hanyar Legas-Ibadan ya ci rayuka 10

Mummunar hatsarin mota a hanyar Legas-Ibadan ya ci rayuka 10

- Motar haya mai lamba BD J410 ta yi karo da motar Dangote mai shake da siminti

- Wannan lamari ya faru ne kan titin da ke tsakanin Legas da Ibadan

- Hatsarin ya faru ne sakamakon ganganci da keta dokar tuki da direban motar hayar ya yi

Wani direban motar haya mai lamba BD J410, da ya taso daga Legas ya yi sanadiyar halakan rayukan mutane 10, maza 7 mata 3, cikin mutane 11 da ya ke dauke da su. Wannan mummunar hatsari ya faru ne daidai Alapako/Ogunmakin na titin da ke tsakanin Legas da Ibadan.

Mummunar hatsarin mota a hanyar Legas-Ibadan ya ci rayuka 10
Mummunar hatsarin mota a hanyar Legas-Ibadan ya ci rayuka 10

Direban da ke sheka gudu, ya yi karo gaba-da-gaba da motar kamfanin Dangote wacce ta ke shake da siminti. Motocin masu zuwa da masu dawowa duk su na kan hannu daya ne sakamakon a na gyaran gada a dayan hannun. wannan lamari ya faru ne ranar 9 ga watan Janairu na 2018, da misalin karfe 9 na yamma.

DUBA WANNAN: An cafke wani mutum da laifin yiwa hafsoshin Sojin Najeriya sojan gona

Jami'in Hukumar FRSC, Florence Okpe, wanda ya yi magana da yawun Hukumar, ya yi kira ga iyalan mamatan da su gabato don karban gawawwakin su. Okpe ya kuma ce an samu naira 151,340 da wayoyin hannu guda 10 a wurin hatsarin.

Direbobin motocin guda 2 da fasinja guda 1 sun tsira da rayukan su a inda kuma fasinjar ke karban kulawa a asibiti. Shi kuwa direban motar hayar tserewa ya yi, amma Hukumar FRSC ta samu kamo shi ta kuma danka shi hannun Hukumar 'Yan Sanda.

Okpe ya bayyana cewan direban ba shi da lasisin tuki kuma motar shi ba ta da na'urar kayyade gudu, ga kuma tayoyin motar sun mace. Don haka ne FRSC ta yi kira da a kikaye dokokin tuki da na kan titi. Mun samu wannan labari ne daga jaridar Punch Metro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164