Zargin cin amana ya sanya wani Saurayi ya tafka ma budurwarsa aika aika a jihar Katsina
Kishi aka ce kumallon mata, sai dai a nan kishin namiji aka gani, wanda yayi muni sosai, inda wani Saurayi ya kama budurwarsa, yayi mata yankan rago kan zargin ta rabu da shi.
Zuma Times ta ruwaito Saurayin mai suna Abubakar Sule mai shekarau 23 na zargin budurwarsa Aisha Dikko mai shekaru 21 ta kammala shirin rabuwa da shi, don ta koma wajen wani saurayi na daban.
KU KARANTA: Aiki ga mai ƙare ka: Babban sufetan Yansandan Najeriya ya isa jihar Benuwe kan lamarin tsaro
Hakan ne ya harzuka Abubakar, wanda ya ja Aisha zuwa wani daji a kauyen Tamawa na garin Kurfi, inda ya danne ta yayi mata yankan rago, kuma ya tsere ya barta rai a hannun Allah, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Sai dai cikin ikon Allah, wani matashi ya gano Aisha kwance jina jina, amma da sauran rai a jikinta, daga nan ya garzaya da ita zuwa babban asibitin garin Kurfi, ganin haka ya sanya Yansanda farautar Abubakar, inda ba da dadewa ba suka cika hannu da shi.
Kwamishinan Yansandan jihar, Beseng Gwana ya tabbatar da lamarin, inda yace zasu tasa keyar Abubakar gaban Kotu. “Saurayin ya tsere ne yana tunanin Aisha ta mutu, har sai da matashin nan dan kasa nagari ya ceci rayuwarta.”
Kwamishinan yace da aka tambayi Saurayin dalilin aikata wannan danyen aiki, sai yace kishi ne ya kwashe shi, bayan Aisha ta yi watsi da shi, kuma ma har an sa mata rana da wani.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng