Za mu koyawa Makiyaya masu tada fitina hankali – Inji Janar Buratai
- Shugaban Hafsun Sojin Najeriya yace za su ga karshen rikicin Makiyaya
- Laftana Janar Tukur Y. Buratai ya bayyana wannan ne a Ranar Laraba
- Ana ta faman rikici tsakanin Makiyaya da kuma manoma da ‘Yan Gari
Labarin da mu ke samu game da rikicin Makiyaya da ‘Yan Gari shi ne Rundunar Sojojin Najeriya za tayi maganin Makiyaya da ke tada fitintinu a cikin kasar nan.
Shugaban Hafsun Sojojin kasa na Najeriya Janar Tuku Yusuf Buratai ya bayyana cewa Sojojin sa zu koyawa Makiyaya masu tada fitina hankali. Babban Sojojin yace za su ga bayan wannan rikici na Makiyaya a Najeriya.
KU KARANTA: Sufetan 'Yan Sanda ya wuce Benuwe don kawo karshen rikici
Fadar Shugaban kasa ce ta bayyana wannan ta bakin wani Hadimin Shugaba Buhari watau Malam Bashir Ahmad. Bashir a shafin sa na Tuwita ya tabbatar da cewa Janar Tukur Buratai ya sha alwashin maganin rikicin.
Laftanan Janar Tukur Buratai ya bayyana wannan ne a jiya Laraba a gonar Sojojin Najeriya da ke Garin Giri a Garin Abuja. Ana dai ta faman rikici musamman tsakanin Makiyaya da Manoma a fadin Kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng