Gwamnati ta ki cewa komai kan rashin lafiyar Yaron Shugaban kasa
- Kwanaki Yusuf Buhari yayi wani hadarin babur a Birnin Abuja
- An rasa gane halin da yaron Shugaban kasa yake ciki a yanzu
- Ana kishin-kishin din za a fitar da shi zuwa asibitin Kasar waje
Fadar Shugaban kasa ta gaza cewa uffan game da yaron Shugaba Muhammadu Buhari watau Yusuf da yake jinya yanzu haka a asibiti bayan yayi hadarin babur. tare da wani abokin sa a Yankin Gwarimpa.
Jaridar Daily Trust tace manema labarai sun nemi Lai Mohammed wanda shi ne Ministan yada labarai na kasar yayi magana game da halin da yaron Shugaban kasar yake ciki amma yayi gum da bakin inda yake cewa wannan sirrri ne.
KU KARANTA: An yi ruwan addu'o'i bayan hadarin Yusuf Buhari
Shi ma wani Darektan yada labarai a Ofishin Uwargidar Shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ya gagara yin magana kan rashin lafiyar. Sulaiman Haruna ya nuna cewa bai da hurumin cewa komai kan wannan batun.
Har yanzu dai Gwamnati ba tace komai ba game da halin da yaron Shugaban kasar yake ciki inda ta nemi a kyale iyalin Shugaban kasar ta ji da jinya. A da dai mun ji cewa za a wuce da Yusuf Buhari zuwa wani asibiti a can Kasar Jamus.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng