Gobara a wani gidan 'yan ci-rani a Makkah ta hallaka mutum biyar

Gobara a wani gidan 'yan ci-rani a Makkah ta hallaka mutum biyar

- Gobara ta tashi a wani gidan 'yan ci-rani a garin Makkah na kasa Saudiyya

- Ta yi sanadin salwantar rayukan mutane biyar

- Wasu mutane biyar sun samu raunuka

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN) ya wallafa labarin barkewar wata gobara a wani gidan 'yan ci-rani a garin Makkah dake yammacin kasar Saudiyya.

Wani jami'in hukumar tsaron farar hula a kasar ta Saudiyya ya tabbatarwa da NAN cewar mutane biyar sun mutu sakamakon gobarar, wasu karin mutane sun sami raunuka.

Gidan da gobara ta tashi yana unguwar Shara al-Mujahdeen ne, kamar yadda kakakin hukumar tsaron farar hula, Nayef al-sheriff, ya sanar.

Gobara a wani gidan 'yan ci-rani a Makkah ta hallaka mutum biyar
Gobara a wani gidan 'yan ci-rani a Makkah ta hallaka mutum biyar

Wutar ta fara kama wasu kayan katako ne dake jibge a farfajiyar gidan kafin daga bisani ta fallatsa ya zuwa cikin dakunan da 'yan ci-ranin, akasarinsu daga Afrika, suke zaune da iyalinsu.

DUBA WANNAN: Akwai dalilin da ya saka ni auren mata uku lokaci guda

An shawo kan gobarar daga baya, kuma har yanzu ba'a tantance da mene ne ya haddasa gobarar ba.

Kasar Saudiyya na daga cikin kasashen duniya dake da yawan 'yan ci-rani a duniya.

NAN ta rawaito cewar kungiyar kwadago ta duniya ta yi kiyasin cewar akwai 'yan ci-rani a kalla mutum miliyan tara a kasar Saudiyya a watan Afrilu na shekarar 2013.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng