Rikicin Kwankwaso da Ganduje: Allah ya hada mu a Daka Tsalle, Kwankwaso zai yaba ma aya zaki –Abdullahi Abbas

Rikicin Kwankwaso da Ganduje: Allah ya hada mu a Daka Tsalle, Kwankwaso zai yaba ma aya zaki –Abdullahi Abbas

An cigaba da nuna ma juna yatsa tsakanin bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da na tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso bisa shirin ziyara da Kwankwaso zai kai jihar a ranar 30 ga wata.

Kwamishinan ayyuka na musamman, Abdullahi Sunusi ya bayyana ma magoya baya cewar za’a su yi jifan shaidan nan bada dadewa ba, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

KU KARANTA: Ilimi na cikin mawuyacin hali a Zamfara: Dalibai 24 kacal suka samu nasara a jarabawar NECO

Sunusi ya bayyana haka ne yayin dayake karbar ragamar mulki daga tsohon kwamishinan ayyuka na musamma, Musa Iliyasu Kwankwaso a ranar Litinin 6 ga watan Janairu, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

“Ina gode ma gwamna Ganduje daya bani wannan mukami, inda bayyana ma yan jama’iyya an cire ma kura ta kunkumi. Abokan rigiman mu na cikin gida sun san kan su, sun ce mu hadu a Minjibir sun gudu, sun ce mu hadu a Hawan Daushe sun gudu, Toh Allah ya kai mu kwanan Dangora ko daka tsalle.

“Idan mutum yayi aikin Hajji, akwai lokacin da ake ce ma jifan shaidan, a saurare mu zamu sanar da ranar da za’a yi jifan shaidan idan ya shigo, muna tabbatar muku bamu tsoron komai, kowa yace mana kule, zamu ce masa cas! Bamu hadu a minjibira ba, a dakinsa a gandun albasa ma mu hadu.”

Ga bidiyon a nan:

Idan za'a iya tunawa, tun bayan karbar ragamar mulki daga hannun Kwankwaso ne aka fara samun tsatstsamar dangantaka tsakaninsa da Ganduje.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: