Abuja: Buhari ya jinjina wa NBA a kokarin inganta zaman lafiya da sulhu a arewa maso gabas

Abuja: Buhari ya jinjina wa NBA a kokarin inganta zaman lafiya da sulhu a arewa maso gabas

- Shugaba Buhari ya jinjina wa NBA a kokarin inganta zaman lafiya da sulhu a arewa maso gabas da kudu maso kudu

- Buhari ya ce da gwamnatinsa ba ta yi nasara ba tare da goyon bayan lauyoyin ba

- Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da tsarob da kuma yaki da cin hanci da rashawa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yaba da kokarin kungiyar lauyoyi ta Najeriya, NBA, don kafa kwamitocin aiki don taimakawa wajen inganta zaman lafiya da sulhu a arewa maso gabas da kudu maso kudu.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, shugaba Buhari ya bayyana cewa da gwamnatinsa ba ta yi nasara ba tare da goyon bayan lauyoyin ba.

Shugaban ya yi wannan magana ne a lokacin da jagorancin NBA suka ziyarce shi a Aso Villa da ke birnin a Abuja.

Abuja: Buhari ya jinjina wa NBA a kokarin inganta zaman lafiya da sulhu a arewa maso gas
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Ya bayyana farin cikinsa ga ziyarar kuma ya yaba shugaban NBA, Abubakar Mahmoud, SAN, wanda ya jagoranci tawagar, saboda nuna bajinta wajen kare hakkin 'yan Najeriya da kuma bin doka a kasar.

KU KARANTA: Zaben 2019: Kwankwaso ya fara motsa magoya bayansa

Shugaba Buhari ya jaddadad cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kasancewa wajen samar da tsaro, da sake dawo da dukiya da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

"Dole ne mu kasance masu bin dokoki don kasar ta ci gaba. Kuma ina godiya ga NBA don taimakawa ga ci gaban wannan gwamnati", inji shi.

Shugaban ya ce lauyoyi da dama suna taka muhimmiyar rawa a cikin gwamnatinsa, irin su mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, SAN da sakataren gwamnatin tarayyar, Mista Boss Mustapha da babban mai shari'a na tarayya da kuma ministan shari'a, Mista Abubakar Malami, SAN, da kuma shugaban ma’aikata ga mataimakin shugaban kasa, Ade Ipaye, wandanda duk sun kasance a taron ziyarar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng