Yarinyar tsohon Gwamna ta fito daga gidan yari bayan daurin kwanaki 90
- Makon nan aka saki ‘Diyar wani tsohon Gwamnan Najeriya
- Kemi Omololu-Olunloyo tayi kwanaki 90 daure a gidan yari
- Baiwar Allar tace ya kamata a duba halin da ‘Yan kaso ke ciki
Dazu mu ka samu labari cewa an sako wata fittaciyar ‘Diyar tsohon Gwamnan Jihar Oyo kuma 'Yar jarida Kemi Omololu-Olunloyo daga babban gidan yarin da ke Garin Fatakwal na Jihar Ribas bayan an dauki tsawon lokaci tana tsare a can.
Kemi Omololu-Olunloyo ta bayyana wannan da kan ta bayan ta fito daga gidan kason a jiyan nan Talata. Baiwar Allar tayi watanni kusan 3 cur tana tsare bayan da aka kama ta a shekarar bara. Kemi ta godewa Magoya bayan ta da kokarin su.
KU KARANTA: 'Dan Sarkin Kano ya shiga ofis a matsayin 'Dan Sanda
Bayan ta fito da kimanin karfe 5:00 na yammacin jiya ne ta saki jawabi inda tace gidan yarin na Garin Fatakwal ya cika makil da masu laifi. Misis Kemi tayi kira na musamman ga Gwamnatin Tarayya ta rage mutanen da ke tsare a gidan yarin.
Omololu-Olunloyo ta bayyana wannan ne a shafukan ta na zamani inda tace nan gaba za ta fara rubutu kan halin da ta tsinci kan ta. Kemi tace Jama’a da dama na daure su na fama da cututtuka iri-iri a cikin babban gidan yarin na Fatakwal.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng