APC ta gayyaci PDP muhawara akan zargin almubazzaranci da naira N400bn

APC ta gayyaci PDP muhawara akan zargin almubazzaranci da naira N400bn

- Shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina ya fadawa manema labaru cewa ashirye suke su yi muhawara da PDP akan zargin almubazzaranci da naira N400bn

- Alhaji Bala Musawa ya ce jam'iyyar PDP ta mu su zargin almubazzaranci ne dan hana dumbin yan jam’iyyar PDP canza sheka zuwa jam’iyyar APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Katsina ta gayyaci jam’iyyar PDP yin muhawara akan zargin da ta yi ma gwamnatin jihar Katsina na almubazzaranci da naira biliyan N400bn a cikin watanni 31.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Bala Musawa, yayi wannan kira ne a lokacin da ya zanta da manema labaru a ranar Talata a Katsina.

Ya ce “APC ashirye take tayi muhawara da jam’iyyar PDP akan zargin da ta mata na yin almubazzaranci da naira biliyan N400bn."

APC ta gayyaci PDP muhawara akan zargin almubazzaranci da naira N400bn
APC ta gayyaci PDP muhawara akan zargin almubazzaranci da naira N400bn

“Muna jiran yan jam’iyyar PDP su sanya ranar da suka shirya yin muhawara da mu, za mu tunkare su a duk lokacin da suka shirya ko da rana ko cikin dare.

KU KARANTA : Buhari ya taba yin alkawarin cewa ba zai yi tazarce ba idan ya samu mulki - Jafar jafar

“Muna son su fito da mana da takardu shaida da suka nuna inda gwamnatin jihar Katsina ta karbi naira bilian N400 daga hannun gwamnatin tarayya.

Musawa ya ce jam'iyyar PDP ta yi wannan zargin ne dan hana dimbin yan jam’iyyar PDP canza sheka zuwa jam’iyyar APC.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: