Mulkin Buhari ne ya sa na fara sana'ar fashi da makami - Inji wani kasurgumin barawo

Mulkin Buhari ne ya sa na fara sana'ar fashi da makami - Inji wani kasurgumin barawo

Rundunar 'yan sandan Nageria tayi nasarar kame wasu gaggan 'yan fashin da makami dake sintiri a tsakanin garuruwan Abuja da kuma Kaduna.

Su dai wadannan barayin suna aiwatar da wannan mummunar sanaar tasu ce akan hanyar Abuja zuwa Kaduna kamar yadda muka samu daga majiyar mu.

Mulkin Buhari ne ya sa na fara sana'ar fashi da makami - Inji wani kasurgumin barawo
Mulkin Buhari ne ya sa na fara sana'ar fashi da makami - Inji wani kasurgumin barawo

Legit.ng ta samu cewa haka zalika wasu daga cikin barayin sun bayyana rashin aikin yi da kuma matsananciyar rayuwa da suka tsinci kan su a ciki a matsayin dalilin da yasa suka shiga sata.

Rundunar ‘yan sandar tace ba zatayi kasa a gwiwa ba har sai ta murkushe masu wannan mummunar sanaar cikin kasa.

A baya ma dai mun samu cewa 'yan sandan na Najeriya sun samu nasarar kama wani kasurgumin mai satar mutane a hanyar inda ya bayyana cewa shi har ma jinin mutane yana sha.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng