Sojojin Najeriya sun rugurguza gidan fitaccen mai garkuwa da mutane, Don Wayne (Hotuna)
Jami’an rundunar Sojan Najeriya sun yi aikin rusau a gidan gagararren mai garkuwa da mutanen nan, Don wayne, inda suka yi ma gidan lebur, kamar yadda Rariya ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta shaida cewar a ranar Lahadi 7 ga watan Janairu ne jami’an rundunar Sojan kasa suka samu nasarar bindige Don Wayne har lahira, bayan wani musayar wuta da suka yi da shi.
KU KARANTA: Wata mata ta haɗa baki da masu garkuwa da mutane don a sace yaron kishiyarta, sai dai ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya
Rahotanni sun tabbatar da cewar an kashe mutumin ne a gab da gwamnatin jihar Ribas ke shirin nada shi sarautar sarkin garinsu, wanda hakan ke alanta kyakkyawar alaka dake tsakanin gwamnatin da shi kansa.
A wani labarin kuma jami’an hukumar tsaro ta sirri, DSS, sun yi nasarar cafke wani barawon yara, da wata mata mai kwadayin Duniya da suka hada baki wajen sace yaron kishiyar matar.
Sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya a yayin da barawon yaran ya dauki yaron matar, a maimakon yaron kishiyarta, wanda a yanzu haka yaron ya mutu, bayan neman kudin fansa naira miliyan 2 daga hannun uban yaron.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng