Sai matasa sun jajirce a rayuwar yau - Ajimobi
A ranar talatar da a gabata ne gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya bayyana cewa, yayi sana'ar wankan gawa a yayin da yake matashi domin samun halin biyan kudin makaranta a lokutan da yake karatunsa a kasashen ketare.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron matasan yankin Kudu maso Yamma da aka gudanar a babban birnin Osogbo na jihar Osun.
Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da gwamnan ke gargadin matasa wajen yin kwazo da kuma jajircewa a rayuwa ta yau, ya bayyana musa cewa sai da ya shafe shekaru takwas yana wankan gawa domin samun taro da sisi da zai yi rayuwa akai.
KARANTA KUMA: Bincike: Kasashe goma mafi kankantar farashin man fetur a duniya
Yake cewa, a wancan lokaci abinda iyayensa suka aika masa bai wuci $30 na gaba daya zaman karatunsa, saboda haka dole kanwar naki ta sanya ya shiga neman yadda zai rayu wurjanjan.
Ya kara da cewa, kada matasa su karaya wajen tashi tsaye domin fuskantar rayuwa duba da kalubalai da suke hangowa, inda yace hakan ita kadai ce hanyar gaci a halin yanzu.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng