Yansandan Najeriya sun yi kyan kai, sun yi ram da masu garkuwa mutane su 19
Rundunar Yansandan Najeriya ta samu gagarumar nasara a kokarinta na yaki da masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan, inda a yau suka cafke wasu miyagun barayin mutane su 19 a Kaduna.
Rundunar Yansanda ta musamman a karkashin jagorancin mataimakin kwamishina Abb Kyari ta kama wadannan mutane ne a garin Jere dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
KU KARANTA: Muhimman abubuwa guda 10 da ya zama wajibi Buhari ya yi cikin shekarar 2018
Daga cikin wadanda aka kama akwai Adamu Lawan, Bature Adamu, Kabiru Abubakar, Sani Nasiru, Yahaya Abdullahi, Ahmed Abubakar, Samaila Yahaya, Abubakar Abba, Ahmadu Abdullahi, Buhari Abubakar, Kabiru Abubakar, Sani Umar, Abdulrashid, Ibrahim Sulaiman, Sani Nasiru, Adamu Haruna, Bello Anji, Usman Mohammed, Audu Lawan da kuma Yahuza Yahuba.
Daily Trust ta ruwaito Kaakakin rundunar CSP Jimoh Moshood a ranar Talata 9 ga watan Janairu yana fadin an kama barayin ne bayan an sha artabu da musayar bindiga, tare da kama makamai da suka hada da bindigar AK 47 guda 8, Alburusai da dama, layu da kuma kakin Sojoji.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda sun ceto mutane 4 daga hannun barayin, kuma tuni suka mika su ga iyalansu, daga karshe kuma yace zasu cigaba da bin sawun sauran barayin da suka arce don ganin sun tabbatar musu da hukuncin daya dace dasu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng