Wata mata ta haɗa baki da masu garkuwa da mutane don a sace yaron kishiyarta, sai dai ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya
Matsalar tsaro, musamman na masu satar mutane na cigaba da kamari, inda wani karamin yaro mai shekaru yayi asarar ransa a hannun barayin mutane a lokacin da suka yi garkuwa da shi a jihar Kano.
Wannan lamari mai daure kai ya faru ne a unguwar kofar Ruwa ta jihar Kano, inda wata mata mai suna Wasila Abdullahi ta nemi wani zauna gari banza, Abubakar , tare da bashi kudi don ya sace dan kishiyarta, wanda ta dade da rasuwa.
KU KARANTA: Zanga zangar sako Zak-Zaky: Anyi arangama tsakanin Yansanda da Yan Shi’a
Muryar Amurka ta ruwaito wannan muguwar mata ta shirya haka ne da nufin karbar fansa daga hannun mijinsu, Alhaji Ahmad Aliyu, da suka kai har naira miliyan 2! Amma abin mamaki sai muguntar ya koma kan ta.

Majiyar Legit.ng ta ruwwaito a lokacin da barayin suka dira gidan, sai suka saci yaron matar da ta aikesu, mai suna Usman, daga nan ne dubunsa ta cika, inda matar ta fallasa, har aka kama shi.
Shi kau daga shiga hannun jami’a rundunar tsaro ta sirri, sai ya fara tsibe musu jawabi, inda yace ba yadda bai yi da matar nan akan ba zai iya wannan danyen aiki da ta sa shi ba, amma ta ki, batun da Wasila ta musanta.
Mahaifin wannan yaro, Ahmad Aliyu yace ya kadu matuka da faruwar wannan lamari, sa’annan yana cikin kaduwa da mawuyacin hali sakamakon mutuwar dan na sa.
Daga karshe, shugaban sashin bincike na hukumar DSS na jihar Kano, Rabiu Garba ya bayyana zasu cigaba da gudanar da bincike da bin diddigin lamarin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng