Labari da duminsa: Mayakan kungiyar Boko Haram 57, Sojoji 3 sun mutu yayin musayar wuta
- An yi musayar wuta tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da dakarun sojin Najeriya
- Mayakan kungiyar Boko Haram 57 sun mutu
- Sojoji 3 sun mutu a musayar wutar
Rundunar soji ta Operation Lafiya Dole mai aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno ta rugurguza wasu sansanin mayakan kungiyar Boko Haram dake kauyukan Metele, Tumbun Gini, da Tumbun Ndjamena.
Sanarwar da Sani Kukasheka ya fitar ta ce ya zuwa yanzu dakarun sojin Najeriya sun hallaka mayakan kungiyar Boko 50 kuma sun lalata maboyar su bayan makamansu na yaki da aka kwace.
Kukasheka ya ce, mayakan na kungiyar Boko Haram sun tsere, bayan da suka ji ruwan wuta, sun bar dabbobi da kayan abinci mai yawa a sansanin nasu.
Kazalika ya bayyana cewar mayakan sun yi yunkurin kaiwa ayarin sojojin hari, saidai sun fuskanci tirjiya daga dakarun soji.
DUBA WANNAN: Bidiyo: Hukumar sojin Najeriya ta fitar da takaitaccen faifan bidiyon fafatawarta da mayakan kungiyar Boko Haram
Kukasheka ya ce dakarun sojin sun yi nasarar kwato makamai masu yawa daga wurin 'yan kungiyar Boko Haram da suka hada da; Bindigu, Alburusai, Roket, gurneti da sauransu. Kazalika an samu litattafan addini da suka hada da Qur'ani da hadisai.
Kakakin hukumar sojin ya kara cewar "saidai abin haushi munyi rashin jami'anmu guda hudu yayin da wasu tara suka samu raunuka. Hakan ta faru ne sakamakon wata motar 'yan Boko Haram makare da bamabamai da ta yi arangama da motar sojojinmu, nan take sojoji uku suka mutu. dakarunmu da suka samu raunuka na samun kulawa a asibitin sansanin sojoji dake Munguno, a jihar Borno."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng