Dalilin da ya saka na auri mata uku lokaci guda

Dalilin da ya saka na auri mata uku lokaci guda

- Dattijo, Mohammed Ssemanda, mai shekaru 50 ya auri mata uku rigis a lokaci guda

- Ya ce ya yi haka ne domin ya samu saukin kashe kudi

- Ya ce matan sun amince su aure shi ne saboda suna sonsa

Wani dattijo, Mohammed Ssemanda, mai shekaru 50 a duniya ya auri mata uku rigis a lokaci guda. Auren na Ssemanda ya jawo cece-kuce da yamadidi a dandalin sada zumunta.

Saidai, Ssemanda, dan kasar Uganda ya kare kansa, ya bayyana dalilin da ya saka shi auren mata ukun lokaci guda.

Dalilin da ya saka na auri mata uku lokaci guda
Dalilin da ya saka na auri mata uku lokaci guda

Ssemanda ya ce auren mata ukun a lokaci guda ya fi sauki a kan auren mata uku a lokaci daban-daban. Ya ce neman sauki ne babbar hujjar sa ta auren mata uku saboda bashi da karfin auren mata uku daya bayan daya.

Ya kara da cewa dukkan mata ukun sun amince su aure shi ne saboda suna sonsa kuma basa kishi da junansu, hasali ma yace matan sun hada kansu wajen tallafawa sana'ar sa ta siyar da kayan abinci.

DUBA WANNAN: An tsare wasu 'yan mata 20 tare da iyayensu saboda sun yi cikin shege a makarantar sakandire

Rahotanni sun bayyana cewar Ssemanda ya shafe tsawon shekaru 20 yana zaune tare da daya daga ciki matan da ya aura, Salmat Naluwugge; mai shekaru 48, ragowar amaren nasa sune; Mastulah; mai shekaru 24, da Jameo Nakayiza; mai shekaru 27.

Kazalika wani rahoto ya ce amaren uku sun kasance cikin matukar farinciki yayin shagalin bikinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: