Hukumar tace fina-finan Kannywood ta yafe wa Rahama Sadau

Hukumar tace fina-finan Kannywood ta yafe wa Rahama Sadau

- Hukumar tace fina-finan Hausa ta ce ta yafewa Rahama Sadau

- Za ta cigaba da fitowa a cikin fina-finai

- Shugaban hukumar, Isma'ila Afakallah, ya sanar da hakan

Shugaban hukumar tace fina-finan Hausa, Isma'ila Afakallah, ya shaidawa wakilin kafar watsa labarai ta BBC cewar an yafewa Rahama Sadau tare da bayyana cewar hukumar a shirye take ta fara tace dukkan fina-finan da jarumar ta fito ko kuma ta dauki nauyi.

Afakallah ya ce hukumar ta amince da nadamar da Sadau ta yi, hakan ya saka hukumar yanke shawarar janye dakatarwar da ta yi Mata a shekarar da ta wuce.

Hukumar tace fina-finan Kannywood ta yafe wa Rahama Sadau
Shugaban Hukumar tace fina-finan Kannywood; Isma'ila Afakallah

"Mu 'yan adam ne, kowa kan iya aikata laifi. Kyamar mai laifi ba zata saka Shi ya shiryu ba, dole mu jawo mutum a jika matukar ya aikata laifi kuma ya yarda ya yi kuskure," a cewar Afakallah.

Afakallah ya kara da cewar "Tun a shekarar da ta gabata, ta zo har ofishina ta bani hakuri, na fada mata ta je ta nemi afuwar sarki da gwamna, kuma ta yi hakan, jama'a shaida ne. Bamu da wani uzuri da ya wuce mu yafe mata."

DUBA WANNAN: Rahama Sadau ta tsallake rijiya da baya

Saidai kungiyar masu shirya ta kasa (MOPPAN) ba ta bayyana matsayinta dangane da janye dakatarwar da hukumar tace fina-finan ta yiwa Rahama Sadau ba. Kazalika bata bayyana ko ta janye takunkumin da ta kakabawa Sadau din ba.

Shugaban kungiyar ta MOPPAN, Kabiru Maikaba, ya tabbatar da cewar sun karbi wasikar neman afuwa da Sadau ta aike masu kuma zasu bayyana mataki na gaba da kungiyar za ta dauka.

Yanzu haka Rahama Sadau na kasar Cyprus inda take karatu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel