Rundunar Yansandar jihar Kaduna ta gargadi mabiya akidar Shi’a akan karya doka oda da Kaduna

Rundunar Yansandar jihar Kaduna ta gargadi mabiya akidar Shi’a akan karya doka oda da Kaduna

- Hukumar yansanda jihar Kaduna ta gargadi mabiya akidar Shi'a akan gudanar da muzahara a jihar Kaduna

- Mabiya akidar Shi'a sun gudanar da muzahara a ranar Lahadi a jihar Kaduna bayan gwamnatin jihar ta haramta ayyukan kungiyar

Rundunar yansandar Jihar Kaduna ta gargadi mabiya akidar Shi’a akan gudanar da taruka da zai iya ta da zaune tsaye a jihar Kaduna.

Mai magana da yawun bakin rundunar yansadar jihar Kaduna, ASP Mukhtar Aliyu, ya ce duk wanda aka kama ya karya dokar da gwamnatin Kaduna ta kafa, zai fuskancin fushin hukuma.

Wannan gargadin ya zo ne kwana daya bayan yan Shi’a sun gudanar da muhazara da yansada suka ce gwamnati jihar Kaduna ta haramata.

Rundunar Yansandar jihar Kaduna ta gargadi mabiya akidar Shi’a akan karya doka oda da Kaduna
Rundunar Yansandar jihar Kaduna ta gargadi mabiya akidar Shi’a akan karya doka oda da Kaduna

“Gwamnati ba za ta amince duk wani taro da zai takura wa al’ummar jihar Kaduna ba.

KU KARANTA : Cin hanci da Rashawa : Kotu ta yankewa wani tsohon shugaban karamar hukuma hukuncin shekaru 6 a gidan Kaso

Aliyu yace matasan kungiyar Shia sun gudanar da muzahara da gwamnati jihar Kaduna ta haramta a ranar Lahadi akan titin Ibrahim Taiwo road zuwa Kano road wanda ya janyo tare hanya da hana mutane zirga-zirga.

Yace rundunar yansanda baza ta amince da gudanar da muhazahara a jihar ba.

Rundunar yansadar jihar Kaduna ta shawarci al’ummar jihar su cigaba gudanar ayyukan su kamar yadda suka saba a kullum saboda jami’an su za su tabbatar da ingantaccen tsaro a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: