Ba zan nemi tazarce ba inji Janar Buhari da bakin sa a 2011

Ba zan nemi tazarce ba inji Janar Buhari da bakin sa a 2011

- Akwai lokacin da Shugaba Buhari ya taba cewa wa’adi daya zai yi a mulki

- Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yace ba a taba yin haka ba

- Ministan Buhari Hajiya Aisha J. Alhassan tace Buhari yace ba zai zarce ba

Mun kwawkulo labari daga wata tsohuwar Jarida ta Daily Trust inda a lokacin yana ‘Dan takarar Jam’iyyar CPC mai adawa Janar Muhammadu Buhari yayi alkawarin yin mulki sau daya ba tare da tazarce ba a Najeriya.

Ba zan nemi tazarce ba inji Janar Buhari da bakin sa a 2011
Buhari da bakin sa yayi alkawarin wa'adi daya a mulki

A Jaridar ta Ranar Lahadin 6 ga Watan Fubrairun 2011, Janar Muhammadu Buhari yayi hira da Jaridar Sunday Trust inda da bakin sa ya bayyanawa Theophilus Abbah na Jaridar cewa idan dai ya samu mulkin kasar to ba zai nemi ya zarce ba.

KU KARANTA: Kokarin Shugaban Kasa Buhari wajen gyara harkar wuta

Muhammadu Buhari na CPC a wancan lokaci yace zai bar harkar siyasar ne saboda ganin cewa shekarun sa sun yi nisa. Buhari yace zai so ya bar harkar siyasa a lokacin da zai yi shekaru 4 a kan karagar mulki don ya haura shekara 70.

Sai dai yanzu ba a sani ba ko Shugaba Buhari zai cika wannan alkawari bayan ya samu mulki a 2015 karkashin APC. Kan ‘Yan APC ya rabu inda wata Minista ta ke ganin haka amma Gwamnan Kaduna El-Rufai yace babu wannan maganar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng