Wani dan shekaru 30 ya zakkewa mahaukaciya a jihar Gombe
Wani zauna gari banza dan shekaru 30 ya gurfana a gaban babbar kotun majistare ta jihar Gombe, bisa laifin fyade wata mata 'yar shekaru 46 dake fama da cutar tabuwar hankali.
Sufeto Bako Shekari, jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa, wanda ake zargi Mustapha Adamu, ya afka dakin matar ne dake unguwar Jakada a tantagwaryar birnin Gombe a ranar 12 ga watan Dasumba, 2017, inda yayi mata ta karfi wajen samun cikakkiyar masaniyar matancinta.
Sai dai a yayin gudanar da zaman, kotun ba ta kama Mustapha ta laifin da ake tuhumar sa ba, inda jami'in dan sandan ya roki kotu ta kara basu lokaci domin karo binkice tare da gabatar da kwararan dalilai a gaban ta.
KARANTA KUMA: 'Yan ta'addan Boko Haram 1,050 sun miƙa wuya ga dakarun soji a gabar tafkin Chadi da Monguno
Alkalin kotun, Babayo Abba Usman, ya daga sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Janairun wannan sabuwar shekarar, ya kuma bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan kaso.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng