2019: Ooni na Ife ya kalubalanci matasan Najeriya game da shugabancin kasar
- Ooni na Ife ya kalubalanci matasan Najeriya game da harkokin siyasa da shugabancin kasar
- Sarkin ya ce matasan su fara ganin kansu a matsayin shugabannin yau ba na gobe ba
- Ooni ya bayyana cewa dattawan kasar ba za su bar shugabancin kai tsaye haka nan ba zai matasa sun tashi tsaye
Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi, Ojaja na II a ranar Asabar da ta gabata ya bukaci matasan Najeriya su kusa kai a harkokin siyasa a kokarin ciyar da kasar gaba da kuma fara ganin kansu a matsayin shugabannin yau.
Legit.ng ta tattaro cewa, sarkin ya kalubalanci matasan su yi watsi da ikirarin cewa su ne "shugabannin gobe", ya ce, wannan kalaman yana kashe karfin gwiwar matasa wanda ya kamata a yi watsi da ita a shekarar 2018.
Ogunwusi ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na sabuwar shekara ta 2018 wanda ya fito daga hannun babban daraktan harkokin yada labarai da kuma hulda da jama’a, Ambasada Musa Olafare.
Ya kuma nuna juyayi ga shugaba Muhammadu Buhari da iyalinsa, game da lafiyar dansa, Yusuf Buhari, wanda ya yi hatsari a zaman babur a Abuja.
KU KARANTA: Malaman makarantun Firamare a Kaduna sunyi ma El-Rufai tawaye (hotuna)
"Dole ne matasan Najeriya su 'yantar da kansu daga ikirarin cewa su ne shugabannin gobe. Yanzu ana samu yawan matasa a shugabanci a duk faɗin duniya kuma bai kamata Najeriya ta kasance a baya ba, amma gaskiyar magana ita ce, dattawan kasar ba za su bar shugabancin kai tsaye haka nan ba”.
"Matasan Najeriya da kansu zai sun yi tsaya daka musamman a harkokin siyasa idan suna so a dauki su da gaske”.
"Firaministan Justin Trudeau na kasar Kanada yana da shekaru 45, Emmanuel Macron na kasar Faransa, 40, Kim Jong Un na Koriya ta arewa, 35, Jacinda Ardem na New Zealand, 37, yayin da Firaminista na Estonia, Juri Ratas yana da shekaru 39”.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng