An tsare wasu 'yan mata 20 tare da iyayensu saboda sun yi cikin shege a makarantar sakandire
- An tsare wasu 'yan mata 20 saboda sunyi cikin shege
- Kwamishinan ilimi ne ya bayar da umarnin tsare daliban da iyayensu
- Masu kare hakkin bil'adama sun ga baikon wannan mataki da kwamishinan ya dauka
Kwamishinan ilimi a yankin Tandahimba dake arewacin kasar Tanzania ya bayar da umarnin tsare wasu 'yan mata 20, 'yan kasa da shekaru 20, tare da iyayensu saboda sun yi cikin shege a makarantar sakandire.
Saidai kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ga baikon wannan mataki da kwamishinan ilimin ya dauka, tare da bayyana cewar wadanda suka yiwa yaran ciki ya kamata a kama.
An bayar da belin 'yan matan da iyayensu daga baya.
Kafar watsa labarai ta Citizen a kasar ta Tanzania ta wallafa cewar wani jami'i a gundumar yankin, Muhammed Azizi, ya ce suna neman mazan da suka yiwa 'yan matan ciki. Kazalika ya sanar da cewar 'yan mata 55 dake makarantun sakandire aka yiwa ciki a shekarar da ta gabata.
DUBA WANNAN: Cikin Hotuna: Mataimakin gwamnan jihar Yobe ya gina makarantar marayu da kudinsa a Potiskum
Da yake karin bayani a kan kamun da aka yiwa 'yan matan da iyayensu, Azizi, ya ce anyi hakan ne domin samun bayanai da zasu kai ga gano mazan da suka yiwa yaran ciki domin kawo karshen yawaitar samun cikin shege tsakanin 'yan matan dake karatu a sakandire.
Wannan batu na cikin shege ya mamaye kafafen yada labarai a kasar ta Tanzania a 'yan kwanakinnan.
Shugaban kasar Tanzania, John Magufuli, ya taba furta cewar kada a kara karbar duk yarinyar da ta haihu a makarantun kasar. Kalaman da 'yan siyasar kasar suka ce ko kadan bai dace ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng