Tsohon mai ba Jonathan shawara, Ahmad Gulak zai koma Jam'iyyar APC
- Mista Ahmad Gulak ya sauya sheka daga PDP zuwa Jam’iyyar APC
- ‘Dan siyasar ya zargi Ahmad Makarfi da kashe Jam'iyyara adawar
- Tsohon mai ba Jonathan shawara na neman kujera a Jam’iyyar APC
Labari ya kai gare mu cewa Babban mai ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a da a game da harkokin siyasa watau Ahmad Gulak ya fice daga Jam’iyyar PDP yana kuma shirin komawa APC.

Asali: Twitter
Ahmad Gulak ya bayyana wannan sauyin shekan na sa ne kwanan nan a wani taro inda ya zargi PDP da yin kama-karya musamman a Jihar Adamawa. Gulak ya zargi tsohon Shugaban Jam’iyyar Ahmad Makarfi da mutanen sa da murdiya.
KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi wani muhimmin nadi a Gwamnatin sa
Gulak yace sauke Shugabannin PDP a Jihar ta sa ta Adamawa da Ahmad Makarfi yayi lokacin yana rikon kwarya ne ya sa dole ya bar Jam’iyyara adawar. Mista Gulak yace dinbin Jama’a za su bi shi zuwa Jam'iyyar APC a Garin Yola da ke Jihar.
Manyan PDP dai sun ce gara da Gulak ya bar Jam’iyyar don kuwa sun matsu da su jefar da kwallon mangoro su huta da kuda. Ana tunani tsohon mai ba Shugaba Jonathan shawarar zai nema kujerar Mataimakin Gwamna ne a Jam’iyyar APC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng