Shugaban kasa ya gana da Gwamnan Adamawa da tsohon Gwamnan Bayelsa

Shugaban kasa ya gana da Gwamnan Adamawa da tsohon Gwamnan Bayelsa

- Shugaba Buhari ya sa labule da Gwamnan Adamawa Bindow

- Shugaban Kasar kuma ya gana da tsohon Gwamnan Bayelsa

- Bakin sun iso Fadar Shugaban kasar ne da rana tsakar yau

Labari ya zo mana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Gwamnan Jihar Adamawa Jibrin Bindow da tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Mista Timipre Sylva a yau Litinin dinnan a ofishin sa a Birnin Tarayya Abuja.

Shugaban kasa ya gana da Gwamnan Adamawa da tsohon Gwamnan Bayelsa
Shugaba Buhari ya gana da Bindow da Sylva

Shugaban Kasar ya gana da manyan 'Yan Jam'iyyar APC ne a Fadar Shubaban kasa na Aso Villa a yau dinnan da kimanin karfe 12:00 na rana. Gwannan dai ya sa labule ne tsakanin sa da manyan bankin na sa wanda kusan su ne farko a wannan makon.

KU KARANTA: An kai wa 'Yan Shia hari da barkonon tsohuwa

Jaridar The Nation ce ta rahoto wannan. Sai dai har yanzu babu wanda ya san wainar da ake toyawa tsakanin Shugabannin a Fadar na Aso Villa. Majiyar mu daga Fadar Shugaban kasar tace a ware Shugaban yake ganawa da Gwamna Bindow da Sylva.

Kawo yanzu dai ba mu li labarin an gama tattaunawar da za ayi ba. Timipre Sylva ya kara neman takarar Gwananan Jihar Bayelsa a kwanakin baya inda ya sha kashi hannun Gwamna Seriake Dickson na Jam'iyyar PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng