Za mu ga karshen ‘Yan Boko Haram duk da ‘yan hararen da su ke kai wa – Buratai

Za mu ga karshen ‘Yan Boko Haram duk da ‘yan hararen da su ke kai wa – Buratai

- Shugaban Hafsun Sojin kasa Buratai ya ziyarci Sojin Najeriya

- Buratai ya nemi Sojojin Kasar su karasa ragowar ‘Yan ta’adda

- Janar Tukur Buratai yace kwanakin Boko Haram sun zo karshe

Dazu mu ka samu labari cewa Rundunar Sojin ta aika wani rikakken mai kashe Jami’a lahira. Yanzu kuma mu ke jin Shugaban Rundunar Sojojin Kasar ya sha alwashin ganin karshen ‘Yan Boko Haram.

Za mu ga karshen ‘Yan Boko Haram duk da ‘yan hararen da su ke kai wa – Buratai
Idan mu ka dage za mu karasa ‘Yan Boko Haram inji Janar Buratai

Shugaban Rundunar Hafsun Sojojin Najeriya Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai yace kwanakin ‘Yan ta’addan Boko Haram sun zo karshe a Duniya don kuwa kwanan nan Sojojin Kasar za su ga bayan su har abada.

KU KARANTA: Yadda aka samu shugabanni 5 cikin mako 2 a Argentina

Janar Buratai yayi kira ga Sojojin kasar da su zage dantse wajen yakar ragowar ‘Yan ta’addan na Boko Haram. Babban Sojan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya kai ziyara zuwa Hedikwatar Sojojin da ke Munguno.

Shugaban Hafsun Sojin Kasar TY Buratai ya nemi jajircewan Sojojin sa wajen ganin an gama da ‘Yan ta’addan da su ke rage a Yankin duk da irin ‘Yan hare-haren da su ke kai wa cikin ‘yan kwanakin bayan nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng