Abin nema ta samu: DPR ta raba kyautar man fetur lita 2,000 ga masu motoci a Kaduna

Abin nema ta samu: DPR ta raba kyautar man fetur lita 2,000 ga masu motoci a Kaduna

- DPR ta raba kyautar man fetur lita 2,000 ga masu motoci a Kaduna

- Wannan man fetur mallakar gidan man na SUL Nigeria Limited wanda ke unguwar Rigachikun ne

- Shugaban tawagar DPR ya ce wannan wani takunkumi ne don hana sauran gidajen man

Sashen harkokin albarkatun man fetur wato DPR reshen yankin arewa ta yamma ta raba kyautar lita 2,000 na man fetur ga masu motoci a Kaduna.

Mista Ibrahim Chiroma, shugaban tawagar haɗin gwiwar DPR, ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa an sami man fetur ne inda aka taskace su a gidan man na SUL Nigeria Limited wanda ke unguwar Rigachikun.

A cewarsa, masu gidan man fetur na sayar da samfurin ga ‘yan ‘black market’ a cikin dare kuma duk da gargadin da aka yi basu daina ba.

Abin nema ta samu: DPR ta raba kyautar man fetur lita 2,000 ga masu motoci a Kaduna
Layin man fetur

Chiroma ya ce tawagar hadin gwiwar tare da mambobi daga dukkan hukumomin tsaro basu da wani zaɓi ila su kwashe samfurin kuma su ba shi kyauta ga masu motoci.

KU KARANTA: Jaridu na Najeriya: Abubuwa 10 da ya kamata ku sani a wannan safiyar ranar Lahadi

Ya ce za su iya rusa bakin famfon gidan man a matsayin wani takunkumi don hana sauran gidajen man fetur.

Chiroma ya jaddada cewa, wannan wani yunkuri ne na kawo karshen matsalar man fetur a kasar.

Legit.ng ta ruwaito a baya cewa DPR ta riga ta sayar da lita 17,700 na man fetur ga masu motoci a Zaria da Kaduna wanda wasu gidajen man suka ki sayarwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: