Illolin dake tattare da yi wa Mata kaciya
- Masana sun bayyana illolin dake tattare da yi wa Mata kaciya
- Ana yiwa Mata kimanin miliyan 33 kaciya duk shekara
- Kungiyoyi da hukumomin lafiya na cigaba da fadakarwa a kan illolin yin kaciya ga 'ya'ya Mata
Anyi kiyasin ana yiwa Mata kimanin 125 kaciya duk shekara a fadin duniya. A Najeriya kimanin yara Mata miliyan 33 ake yiwa kaciya duk shekara, kamar yadda wani rahoton binciken kungiyar kare hakkin yara ta duniya (UNICEF) ya tabbatar.
Saidai masana lafiya sun bayyana cewar kaciyar mata ce babban abinda ke jawo cutar yoyon fitsari, rashin haihuwa, tabin hankali, kanjamau, da cututtuka masu yawa.
Wata kungiyar wayar da kan matasa domin samun ingantacciyyar rayuwa (LIFE) sun shirya wani taro domin zakulo tare da wayar da kan mutane a kan illolin yiwa Mata kaciya.
Wata likitar lafiyar al'umma, Dakta Temitope Ajayi, ta ce yiwa Mata kaciya na jawo masu jimawa suna nakuda kafin haihuwa, kuma da yawan Matan da aka yiwa kaciya basa iya haihuwa ba tare da an kawo masu agaji ba.
DUBA WANNAN: Mun samu rahotannin rigingimun aure da na karuwanci 98,217 a 2017 - Kano Hisbah
Ajayi ta kara da cewar yin kaciya ga 'ya'ya Mata na taba tunaninsu saboda ukubar da suke sha yayin kaciyar.
Jagoran kungiyar LIFE, Joseph Afam, ya bayyana rashin dacewar yin kaciya ga Mata ko don saboda azabtarwa da ake yi gare su ta hanyar saka abu mai kaifi a yanke wani bangare na farjin su. Ya ce matan kan ka samu firgicicewar tunani dake jawowa tunaninsu tawaya.
Ya bayyana cewar zasu cigaba da wayar da kan mutane domin ganin an rabu da wannan muguwar al'ada.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng