An samar da maganin makanta na farko a duniya

An samar da maganin makanta na farko a duniya

- An kirkiri maganin makanta na farko a duniya

- Yana magance makanta koda ta gado ce

- Maganin na da matukar tsada

Wani kamfanin hada magunguna 'Spark' ya samar da wani maganin makanta na farko a tarihin duniya.

Maganin da kudinsa ya kai dalar Amurka $850,000 kwatankwacin Naira miliyan N300, zai magance makanta koda kuwa ta gado ce.

An samar da maganin makanta na farko a duniya
An samar da maganin makanta na farko a duniya

Masana kasuwar magunguna a duniya sun ce maganin shine mafi tsada yanzu haka a duniya.

DUBA WANNAN: Cikin Hotuna: Mataimakin gwamnan jihar Yobe ya gina makarantar marayu da kudinsa a Potiskum

Duk da tsadar kudin maganin, kamfanin Spark ya ce a hakan ma ya rage kudin maganin daga farashinsa na farko, dalar Amurka miliyan daya $1M zuwa dubu dari takwas da hamsin saboda amincewar da kamfanonin inshora suka yi na biyawa marasa lafiyar ido zunzurutun kudaden da kuma bawa jama'a damar sayen maganin.

A watan Disambar 2017 aka amince da 'Luxturna' a matsayin maganin makanta koda kuwa an gada ne daga iyaye da kakanni.

Maganin zai iya dawowa da mutum ganinsa koda kuwa ya dade da makancewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng