Assha: Mai gida yayi wa Surukar sa ciki a Jihar Nasarawa
- Wani mutumi mai shekaru 45 yayi wa surukar sa ciki a Nasarawa
- Mahaifiyar Uwar ta sa ta dawo gidan su ne don taya su aikin gona
- Matar ta sa da ya dade su na zaman aure ta ji takaicin wannan abu
Kwanan nan mu ka ji wani labari na wani Mutumi mai shekaru 45 a Jihar Nasarawa da ya bar Surukar sa da ciki. Wannan mutumi dai yace aikin Shaidan ne kuma yana nema a zubar da cikin yanzu haka.
Jaridar Sun ta rahoto labarin wani mutumi mai suna John Ulaha da yayi wa Uwar Matar sa ciki kwanan nan a Karamar Hukumar Awe ta Jihar Nasarawa. Abin ya faru ne bayan da Mai dakin sa ta nemi Uwar ta ta dawo gidan su da zama kwanakin baya domin taya su aiki.
KU KARANTA: Amfanin da tashar ruwa da Shugaba Buhari ya bude za tayi wa Arewa
Wannan mutumi a nan ne ya samu damar kwanciya da wannan mata da dama tuni Mijin ta ya rasu. Tace dai ba ta taba tunanin za tayi daukar ciki ba don haka ne ta saki jikin ta, ta cigaba da tarawa da Mijin ‘Diyar ta sau da yawa har Allah kuma yayi rabo ya shiga.
Shi dai wannan mutumi yace abin ya dame sa kuma tun lokacin da Matar sa ta fallasa abin ya shiga wani halin takaici. Ulaha yana nema ne yanzu a samu a zubar da wannan ciki. Matar ta sa tace dama wata Budurwa yaje ya samu a waje don abin da matukar kunya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng