Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

- Sarkin Kara na Zariya da Hakiman sa sun yi hawan daban dokin kara

- Sun sha ado kuma sun yi kamanceceniya matuka da hawan da Sarakuna ke yi

- Sarkin Karan ya yi koyi da Sarkin Zazzau a inda shi ma ya hau keken doki

A yau Asabar, 7 ga watan Janairu na 2018 ne Sarkin Karan Zariya na Masarautar Zazzau na Jihar Kaduna, tare da Hakiman sa, su ka yi hawan daba a dawakan kara. A kwanakin baya ne Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris, ya nada Sarkin Karan Zariya. Shi kuma Sarkin Karan sai ya nada yara sa'annin sa a matsayin Hakiman sa.

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

KU KARANTA: Sojoji sun yiwa shugaban kungiyar Boko Haram babban lahani

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

A hawan na su, sun yi kamanceceniya matuka da hawan daba da na Bikin Sallah da Sarakuna ke yi. Don kuwa Sarkin Karan, keken doki ya hau, ya na mai koyi da Sarkin Zazzau.

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Hakimai kuma da tawagar su sun sha ado cikin kayaki na sarauta. A gaban su kuma ga masulta,yan kwalkwali, masunta,yan banga, 'yan zagi, Dogarai, 'yan babule, 'yan sulke da 'yan bindiga.

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Su kuma makada su na yin kida, mubusa da 'yan algaita su na yin busa, su kuma buwara su na zabga kirari. Can kuma fadan Sarki, Gwamnan Kara ya na zaune ya na karban gaisuwa. Abun dai gwanin ban sha'awa.

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau
Yara sun yi hawan Daba a Birnin Zazzau

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164