Sabon jirgin kasa zai rika tashi sau 4 a kowace rana – Gwamna El-Rufai

Sabon jirgin kasa zai rika tashi sau 4 a kowace rana – Gwamna El-Rufai

- Gwamnan Kaduna ya godewa Gwamnatin Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya kawo jiragen kasa zuwa Garin Kaduna

- Yanzu za a rika jigilar fasinjoji sau 4 a kowace rana ta Allah

Kwanan nan ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a Jihar Kaduna wanda daga ciki akwai karin jiragen Kasa da ke daukar fasinjoji zuwa Birnin Tarayya Abuja.

Sabon jirgin kasa zai rika tashi sau 4 a kowace rana – Gwamna El-Rufai
Gwamna El-Rufai ya jinjinawa Gwamnatin Buhari

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai a shafin sa na Facebook, ya yabawa Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari na kawo cigaba a Jihar. Gwamnan ya kuma yabawa Ministan sufuri na Kasar Rotimi Amaechi da mutanen Ma’aikatar sa.

KU KARANTA: Amfanin da tashar ruwa da Shugaba Buhari ya bude za tayi wa Arewa

Yanzu haka Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa za a riga jigilar fasinjoji sau 4 a kullum yanzu. Za a riga daukar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna da karfe 7:00 da 9:50 na safe. Sannan kuma da karfe 2:20 na rana da yammacin karfe 6:00.

Sannan kuma za a rika zaryar fasinjoji daga Kaduna zuwa Abuja da karfe 6:40 da kuma 10:35 da kowace safiya. Za kuma a rika daukar fasinjoji da karfe 2:00 na rana da kuma karfe 6:00 na yammacin kullum Inji Gwamnatin na Jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng