Yan bindiga sun kashe mutane 5 a sabon harin da aka kai jihar Rivers
- An kai sabon hari a wani gari dake jihar Rivers
- Harin ya yi sanadiyan mutuwar mutane biyar a garin Egbeda dake karamar hukumar Emohua
- An kawo cewa wasu yan fashi ne suka kai hari ga al’umman garin a safiyar yau
Yan kwanaki kadan bayan an kashe mutane 17 a ranar sabon shekara a jihar Rivers, wasu yan bindiga sun kashe mutane biyar a garin Egbeda dake kamar hukumar Emohua dake jihar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai hari yankin amma dai wasu jami’an tsaro sunyi nasarar koransu bayan sun billo daga daji.
Rundunar yan sandan ta kuma ce mutane biyu ne kawai suka mutu a harin.
Wata majiya daga garin ta ce yan bindigan sun sanya bakaken wanduna da riga da kuma jan wula.
Amma sun tsere bayan sun gano cewa wasu sojoji na biye da su a dajin.
Majiyar ta kuma bayyana cewa harin ya afku ne da safe a lokacin da mazauna garin ke shirye-shiryen fita harkokinsu na yau da kullun.
Har ila yau da yake tabbatar da al’amarin kwamishinan yan sandan jihar Rivers, Ahmed Zaki, yace mutun daya kawai aka kashe a Unyeada dake karamar hukumar Andoni na jihar.
KU KARANTA KUMA: Ba za mu gaji ba har sai sauran yan matan Chibok sun kubuta - BBOG
Zaki ya ce yan iskan sun zo ne akan babur, sannan kuma harbi mutun daya har lahira a Egbeda.
Ya kuma bayyana cewa yan sanda sun tsaurara tsaro a yankin domin guje ma sake afkuwar irin wannan al’amari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng