Kishin Kishin: Ana tunanin Sheikh Isa Ali Pantami zai tsaya takarar gwamnan Gombe

Kishin Kishin: Ana tunanin Sheikh Isa Ali Pantami zai tsaya takarar gwamnan Gombe

Ana cigaba da rade-raden cewa shahararren malamin addinin islama din nan mai suna Sheikh Isa Ali Pantami zai tsaya takarar gwamnan jihar sa ta Gombe a zabe mai zuwa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kiraye-kiraye ke dada kara yawaita daga jama'ar jihar da dama zuwa ga shugaban ganin cewa lokacin ya matso.

Kishin Kishin: Ana tunanin Sheikh Isa Ali Pantami zai tsaya takarar gwamnan Gombe
Kishin Kishin: Ana tunanin Sheikh Isa Ali Pantami zai tsaya takarar gwamnan Gombe

Legit.ng ta samu dai cewa a yayin daya daga cikin wannan kiraye-kirayen da ake yi masa, wani bawan Allah da ake kira da Malam Lawal Mu'azu Bauchi ya wallafa a shafin sa na Facebook, malamin ya mayar da martani.

Sai dai a martanin malamin ya nuna matukar shakkun sa game da hakan inda ya nuna cewa yana tsoron shugabanci musamman ma na gwamna da yake da matukar girma.

Haka nan kuma malamin ya bayyana cewa duk da haka akwai yiwuwar kowa ya bayar da gudummur sa domin kawo cigaba mai ma'ana.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng