Ba za mu gaji ba har sai sauran yan matan Chibok sun kubuta - BBOG

Ba za mu gaji ba har sai sauran yan matan Chibok sun kubuta - BBOG

‘Yan Kungiyar nan ta BringBackOurGirls masu kokarin ganin an ceto ‘yan matan Chibok da aka sace a makaranta tun lokacin shugaba Jonathan sun jajirce a kan bakan su.

Sun ce ba za su saduda ba har sai sauran yan matan sun kubuta daga hannun kungiyar yan ta’addan Boko Haram.

Daya daga cikin 'yan kungiyar ta BringBackOurGirls Morocco Ibrahim, ya bayyana cewa wannan labari ne da ya sanya su farin ciki, tare da godewa gwamnati kan kokarin da take yi na kubutar da 'yan matan.

Ya kara da cewa, kungiyar su ba za ta gajiya ba har sai lokacin da aka kubutar da dauran 'yan matan 112 da suka rage hannun mayakan na Boko Haram.

A jiya ne dai Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da kungiyar 'yan ta-da-kayar-baya ta Boko Haram, Manjo Janar Nicholas Ibe Rogers ya ce dakarunsa sun kubutar da wata 'yar makarantar sakandaren Chibok wadda ta shafe kusan shekara 4 a hannun Boko Haram, a ranar Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Allah ya tona asirin wasu korarrun sojoji da suka saci mota a Kano

Wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da manema labara na rundunar Kanal Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce an gano yarinyar ne a garin Pulka da ke jihar Borno.

A lokacin da aka gano ta tana tare da wata yarinya mai suna Jamila Adams, mai kimanin shekara 14 da kuma wani jariri kuma yanzu haka sojoji suna kulawa da su tare da ba su magunguna, in ji sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng