'Yan sandan Najeriya sun kama wasu sojoji da motar sata a jihar Kano
Jami'an SARS masu yaki da 'yan fashi da makami a Jihar Kano sun yi nasarar kame barayin mota sanye da kakin sojoji.
Jami'an SARS din sun yi nasarar kame 'yan fashin ne bayan sun yi fashin sabuwar mota kirar Hilux daga garin Fatakwal kan hanyar su ta wucewa da ita Jamhuriyar Nijar domin batarwa.
Legit.ng ta samu cewa Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Magaji Musa Majia, ya ce 'yan fashin dake sanye da kakin sojoji sun bayyana cewa su korarrun sojoji ne da aka kora lokacin da suka gujewa yaki da ta'adacci a garin Bama na Jihar Borno cikin shekara ta 2016.
Dakarun na SARS dake nan jihar Kano tare da hadin gwiwar jami'an SARS na jihar Katsina, sun samu rahotan 'yan fashin ne daga jami'an SARS na Jihar Rivers.
Wannan nasara da rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta fara samu a wannan sabuwar shekara ta 2018, alamu ne na ta shiga shekarar da kafar dama wajen yaki da masu aikata miyagun laifuka musamman 'yan fashi da makami.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng