Daliban Sheik Zakzaky suna neman hakkinsu bisa kisan gillar da aka yi wa iyayensu
- Almajiran Sheik Zakzaky sun gudanar da zanga-zangar neman hakkinsu bisa kisan gillar da jami’an tsaro suka yi wa iyayensu
- Yaran sun bukaci a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda gwamnati ke ci gaba da tserewa
- Almajiran sun dauko zanga-zangar ne daga kofar babban kotun tarayya da ke Maitama Abuja har zuwa kofar ma'aikatar Shari'a ta kasa
Daruruwan yara kanana kuma daliban shugaban kungiyar Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda a halin yanzu yana rufe sun gudanar da zanga-zangar lumana inda suka bukaci a biya su hakkinsu bisa kisan gillar da jami’an tsaron Najeriya suka yi wa iyayensu da kuma ci gaba da tsare jagoran hakar Musulunci Sheikh Ibrahim Zakzaky da gwamnati ke ci gaba da yi.
Zanga-zangar wanda daliban suka dauko daga kofar babban kotun tarayya da ke Maitama Abuja har zuwa kofar ma'aikatar Shari'a ta kasa, inda suke kira da babban murya a kan bukatar shugaban wannan wurin ya fito domin ya tarbe su ya kuma saurari kokensu a kan abin da suke dauke da shi.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, har lokacin da wadannan yara suka kammala ba su samu tarbo daga ministan Shari'a Abubakar Malami ba, inda daliban suka gabatar da takardar su ga sakataren ma’aikatar kana kuma suka gangara zuwa dandalin 'yanci na Unity Fountain.
KU KARANTA: Zaben 2019: Wasu sun fara shirin fitowa takarar Shugabancin Najeriya
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng