Gwamnatin tarayya tana da zabi uku akan N145 na farashin man fetur

Gwamnatin tarayya tana da zabi uku akan N145 na farashin man fetur

A yayin da gwamnatin tarayya take ta cukucukun shawo kan matsalar karanci da rashin wadatar man fetur a fadin kasar nan, kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin gudanar da binciken diddigi wajen gano ainihin bakin zaren tare da magancewa farad daya, yana yunkurin yin la'akari akan wasu zabuka uku.

Kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa yana da zabi na cire takunkumi akan dillalan man fetur na wajen shigo da man fetur cikin kasar nan kuma su sayar a farashin da suka ga dama a yayin da kamfanin man fetur na kasa wato NNPC zai ci gaba da sayarwa a farashin N145 na kowace lita guda.

Karamin ministan man fetur; Dakta Ibe Kachikwu
Karamin ministan man fetur; Dakta Ibe Kachikwu

Karamin ministan man fetur na kasa, Dakta Ibe Kachikwu shine ya bayyana hakan a farfajiyar majalisar dattawa a yayin da yajagoranci kwamitin a ranar Alhamis din da ta gabata.

KARANTA KUMA: Kotu ta jefa wata makauniya gidan kaso bisa laifin zagin masarautar kasar Thailand

Yake cewa, akwai zabi na yiwa dillalan man fetur wata yarjewa ta musamman akan canjin dalar Amurka da zasu iya shigo da man fetur kuma su sayar da a farashin N145 na kowace lita guda.

Sai kuma zabi na karshe shine gwamnatin tarayya ta kawo wata sabuwa hanya ta musamman ta kyautatawa akan tsarin haraji da zai ƙarfafawa dillalan man fetur wajen ci gaba da sayarwa akan wannan farashi.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng