Wahalar man fetur yayi kamari a Yankin Arewacin Najeriya
- Ana cigaba da fama da wahalar man fetur a Najeriya
- A wasu wurare lita ya haura sama da N250 a Arewa
- Sai dai a manyan Birane an rage layin man a gidaje
Har yanzu ana matukar wahalar man fetur a Najeriya musamman Yankin Arewa maso gabashin Kasar kamar yadda binciken da da dama da ‘Yan Jaridan Najeriya su kayi ya nuna cikin kwanakin nan.
A wasu wurare irin Garin Borno ana saida galan din mai a kan kudi har N2500 yayin da gidajen mai da dama ke garkame har yanzu a Yankin. Litar mai dai tana kai sama da N250 a wurare da dama a halin yanzu da ake ciki.
KU KARANTA: ‘Yan kasuwa sun amice su cigaba da saida man fetur a kan N145
A yankin Yobe da Bauchi ma dai ana wahala kwarai da gaske. Har a irin su Kaduna, inda Shugaban kasar ya kai ziyara akwai dogayen layin mai. Gwamnati dai ta yi kokarin rage layin musamman a Legas da kuma Birnin Abuja.
Wani rahoton kuma daga Jaridun kasar nan ya tabbatar da cewa duk da irin sanyin da ake fama da shi, a irin su Jihar Katsina wasu na kwana a layin gidan mai domin su samu mai a motocin su a wannan lokaci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng