An cafke kasurgumin mai garkuwa da mutane a jihar Jigawa
- Jami'an hukumar 'yan-sanda a jihar Jigawa sun kama shugaban masu garkuwa da mutane
- An dade ana neman wannan kasurgumin dan ta'adda
- Hukuma ta ce ya karbi miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa
Hukumar 'yan-sandan Najeriya reshen jihar Jigawa ta ce ta yi nasarar damke wani gawurtaccen shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da suka dade suna addabar mutanen jihohin Jigawa da Bauchi.
Kakakin rundunar hukumar'yan-sanda a jihar Jigawa, SP Abdul Jinjiri, ya sanar da manema labarai a jiya Laraba a garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Jinjiri ya ce "Jami'an mu sun yi nasarar cafke gawurtaccen shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da ake kira Buba, wanda muka dade muna nema ruwa a jallo."
Jinjiri ya kara da cewar kungiyar masu garkuwa da mutane karkashin jagorancin Buba ta dade tana addabar mutanen yankin karamar hukumar Gwaram da kuma wasu sassan jihar Bauchi dake da makobtaka da jihar Jigawa.
DUBA WANNAN: Atiku ba zai samu tikitin takara a PDP ba, inji Omale
"Ya dade yana satar mutane don ko a shekarar da ta gabata saida ya sace mutane a garin Kafin Madaki dake karamar hukumar Gwaram. Ya karbi miliyan uku kuma ya kashe mutanen da ya yi garkuwar da su kuma ya gudu," a cewar Jinjiri.
Buba dan asalin jihar Bauchi ne kuma muna tuhumar sa da aikata laifukan Kisa, hada baki domin aikin ta'addanci, da kuma garkuwa da mutane.
Kakakin ya kara da cewar da zarar sun kammala bincike a kan Buba zasu gurfanar da shi a gaban Kotu domin girbar abinda ya shuka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng